Mene ne corona kuma me zanyi akansa?

Kwayar cutar korona (Coronavirus) wata karamar kwaroce (wacce idanu baya iya gani don kankanta) wacce kan yadu kuma ta haifar da ciwo ga mutane. Korona na da alamomin mura wanda ya hada da tari mai busar da makokwaro, daukewa numfashi, zazzabi, da kuma ciwon jiki. Korona yafi kama bangaren numfashi na jikin dan Adam. Cututtuka da dama basu da hatsari, amma yakan jawo ciwon huhu kuma yakan yi kisa ayawancin lokuta.

Kowa na iya kamuwa da korona. Dattijai da kuma mutane wanda suke da wasu nau’ikan cututtuka kamar ciwon huhu, ciwon daji, ciwon suga suna cikin wanda cutar yafi yima illa.

Korona kan yadu ne daga wanda ya kamu idan yafitar da Numfashi, tari, ko atishawa kusa da mutane, ko akan wani abun ko abinci. Yakan shiga cikin jiki ta baki, hanci, da kuma idanu. Da zarar ya shiga jiki, sai ya fara hayayyafa ya kuma bazu zuwa wasu sassan jiki. Korona kan zauna a jikin dan Adam na tsawon kanaki sha hudu (14) kafin alamominsa su bayyana. Adon haka mutane kan iya kamuwa da korona batare da sun sani ba, har su yada ta ga wasu.

Garkuwan jiki bai iya kashe korona ko magunguna gida. Akan iya hana yaduwar korona ta hanyar rage mu’amular da zai sa mutum ya kamu da ita da kuma yawaita wanke hannu.

Domin kare kai daga cutar, sai a wanke hannu da Sabulu da ruwa. A rika yin hakan koda hannu bai nuna alamun dattiba. Sai awanke da kyau a ruwa na tsawon dakika ashirin da ruwa, a kuma tabbata cewa an cuda kasan yan yatsu and kuma wanke hannu har ya zuwa idon sawu. Wanke hannu da sabulu da ruwa yakan kashe kwayaoyin cuta wanda kila suna manne a hannu. Arika wanke hannu kafin da kuma lokutan da ake dafa abinci har sanda aka gama, indan an fito daga ban daki, kafin aci abince, har lokutan da ake jinyar wani maralafiya, ida an taba dabbobi ko kashin su, haka kuma idan anyi tari, attishawa ko an fyace hanci.

A guji taba idanuwa, hanci, da kuma baki kafin a wanke hannu. Hannun da ya taba wurare daban-daban kan iya dauko kwayar cuta. Da zarar hannu ya dauka to zai iya watsa shi zuwa idanu, hanci ko baki. Daga nan kuma kwayar cutar sai ya shige cikin jiki ya sa ka rashin lafiya.

Yana da matukar muhimmanci mutum ya rage shigewa wanda keyin zazzabi ko tari ko kuma ciwukan da suka shafi huhu. Idan ana tari ko atishawa, to arika kulle baki da hanci da idan sawu na hannu ko asa tishu. Sai asa shi a bola da wuri. Adaina zubda yawu a wurin da akwai mutane.

A rika matsawa akalla mita daya (taku uku) tsakaninka da wani mai tari ko atishawa. Arage tarayya da Wanda ke zazzabi ko tari.

Idan ya kama za kai jinyar wani mai dauke da ciwon zazzabi, tari, ko daukewar numfashi kar a manta asanya abun kariya na fuska ko kyalle mai kyau da za a rufe fuska dashi da kuma kulla da wanke hannaye akai-akai.

Domin kariya daga korona, yafi kyautatuwa a rage cudanya da mutane. Akan iya yada korona da wasu kwayar cutar ta hanyar gaisuwa da hannu kana daga bisani a taba idanuwa da hannun, ko hanci ko baki. Don haka ida an hadu da wasu sai a daina gaisawa da hannu, ruguma ko kuma sumbata. A gaisa da mutane ta hanyar daga musu hannu, ko gyada kai ko a durkusa a gaishesu. Idan kana tunanin akwai korona a unguwarku sai kai zamanka a gida a rage cudanya da mutane.

Azauna a gida idan kana jin alamun ciwo, koda kuwa dan ciwon kaine da kuma mura kadan, har sai ka warke. Idan kana atishawa, ko tari mai sa bushewar makogoro, ko yin numfashi da kyar ko zazzabi to sai anemi ganin likita da wuri hakan ka iya zama wani ciwo ne na bangaren huhu ko kuma wani babban ciwonne.

Camfi da kuma jita-jita game da korona ka iya zama babban matsala kuma hakan na iya jawo asaran rayuka. Kamar misali, shan wani abu kamar bleach ko giya kan iya cutarwa fiye da kariya daga korona. Har labarai da abokai ko yan uwa ka iya zama ba daidai ba ko mai hatsari. Kabi bayanai sahihai daga bangaren kiwon lafiya mafi kusa da ku.

Zaka iya taimakawa wajen yaki da cutar korona ta hanyar watsa wannan sako. A turama abokai da ‘yan uwa musamman ta hanyar WhatsApp
Audiopedia ce ta kawo muku wannan bayanin, Sako na bai daya mai isar da sakon kiwon lafiya. Don samu Karin bayani a www.audiopedia.org